Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 18 sun mutu a hadarin mota a Najeriya
2019-06-09 15:17:25        cri
Kimanin mutane 18 ne suka hallaka a sanadiyyar mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar jihar Ondo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, wani jami'in ne ya tabbatar da hakan.

Femi Joseph, kakakin hukumar 'yan sanda jihar ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce an kwashe gawarwakin mutanen zuwa babban asibitin jihar Ondo dake Akure, babban birnin jihar.

Ya ce hadarin ya faru ne tsakanin wata motar bas mai daukar mutane 18 wacce ke kan hanyarta ta zuwa Abuja, babban birnin kasar, inda suka yi karo da wata babbar motar daukar kaya inda suka yi taho mu gama.

Joseph ya ce, motocin biyu sun yi karo da juna ne a kokarin da suke na kaucewa kananan ramuka dake kan titin, inda daga bisani motar bus din ta kama da wuta kuma babu ko da mutum guda da ya tsira daga cikin motar.

Mace-mace ta sanadiyyar hadarin mota ya neman zama ruwan dare a Najeriya, galibi ana samun hadarin ne saboda lodin kayayyakin da ya wuce kima, da rashin kyawun hanyoyin mota, da kuma tukin ganganci.

Wani rahoton da hukuma ta fitar ya nuna cewa, sama da mutane 100 ne suke mutuwa a kowane wata a sanadiyyar hadduran mota a Najeriya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China