Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gabatar da bayani a kafofin watsa labaru na Koriya ta Arewa
2019-06-19 11:28:27        cri
Kafin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a kasar Koriya ta Arewa, ya gabatar da bayani mai taken "sada zumunta tsakanin Sin da Koriya ta Arewa, da bude sabon babi a zamani" a jaridar Rodong Simun da manyan kafofin watsa labaru na kasar Koriya ta Arewa.

Bayanin ya yi nuni da cewa, a bana ake cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. A matsayin sahihiyar abokiya dake dab da kasar Koriya ta Arewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin Sin ba su canja matsayinsu na raya dangantakar abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da Koriya ta Arewa ba, Sin za ta nuna goyon baya ga shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un da ya jagoranci jam'iyyar da jama'ar kasarsa wajen aiwatar da manufofi da kokarin raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma sa kaimi ga kara samun nasarori kan tsarin gurguzu na kasar.

Bayanin ya yi nuni da cewa, shugaba Xi Jinping yana son yin kokari tare da shugaba Kim Jong-un ta hanyar ganawa a wannan karo wajen tsara shirin raya dangantakar abota ta hadin gwiwa a tsakaninsu, da bude sabon babi na sada zumunta. Ya nuna cewa, ya kamata bangarorin biyu su kara mu'amala da juna don sada zumunta da juna, da kara yin hadin gwiwa don raya dangantakar dake tsakaninsu, da kuma kara yin shawarwari don bude sabon shafi na kiyaye zaman lafiya da na karko a yankin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China