Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasa da kasa sun yaba wa jawabin shugaba Xi Jinping a gun taron kolin CICA
2019-06-17 12:09:05        cri

An gudanar da taron kolin matakan hadin kai da amincewar juna na Asiya karo na 5 wato (CICA) a kasar Tajikistan a ranar 15 ga wata, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. Kasa da kasa suna ganin cewa, jawabin shugaba Xi Jinping ya bayyana ra'ayin Sin wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da wadata a nahiyar Asiya, tare da gabatar da shirye-shirye ga kasashen Asiya wajen kara fahimtar juna, da yin imani da juna, da zurfafa hadin gwiwa, da samun moriyar juna, da kuma bude sabon babi na kiyaye tsaro da samun ci gaba na Asiya.

Direktan sashen nazarin harkokin Sin na cibiyar nazarin siyasa da kafofin watsa labaru ta kasar Masar Imad Azrak ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya hada da batun kiyaye tsaro da samun ci gaba tare, kana ra'ayinsa zai taimakawa wajen raya nahiyar Asiya mai yin imani da juna a fannin siyasa, ta hakan za a daidaita matsalolin rashin daidaito kan tattalin arziki a tsakanin yankunan nahiyar, har ma za a sa kaimi ga samun ci gaba a duk duniya baki daya.

Mai nazari na sashen nazari kan yankin gabas na cibiyar kimiyya da fasaha ta Rasha Vasily Kashin ya bayyana cewa, a cikin jawabin shugaba Xi, ya bayyana fatan Sin na more damar samun ci gaba tare da kasa da kasa, da kara samar da sharadi ga bangarori daban daban wajen shiga kasuwar kasar Sin, wadannan manufofi suna matukar jawo hankalin kasa da kasa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China