Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da Donald Trump bisa gayyatar da aka yi masa
2019-06-19 09:45:56        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a jiya bisa gayyatar da aka yi masa.

Shugaba Trump yana fatan zai sake ganawa da shugaba Xi Jinping a yayin taron kolin Osaka na kungiyar G20, don kara yin mu'amala kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da batutuwan dake jan hankalinsu. Ya ce Amurka ta dora muhimmanci ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da kasar Sin, tare da fatan bangarorin biyu za su kara yin mu'amala don neman hanyoyin daidaita matsalar dake kasancewa a tsakaninsu. Ya yi imanin cewa, dukkan duniya na son ganin Amurka da Sin sun cimma yarjejeniya.

A nasa bangare, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, ana fuskantar wasu matsaloli kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, inda ya ce hakan bai dace da moriyarsu ba. Ya ce Sin da Amurka za su samu moriya idan su yi hadin gwiwa, amma za su samu hasara idan suna adawa da juna. Ya kamata bangarorin biyu su bi ayyukan da suka cimma daidaito a kai, da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu bisa tushen girmama juna da samun moriyar juna. Xi Jinping ya ce, yana son ganawa da shugaba Trump a yayin taron kolin Osaka na kungiyar G20, don yin musayar ra'ayoyi kan batutuwan dake shafar dangantakar dake tsakaninsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China