Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi bayani kan ziyarar shugaban kasar
2019-06-16 18:13:46        cri

Daga ranar 12 zuwa 16 ga wata, shugaban kasar Sin ya kai ziyarar aiki kasashen Kyrghyzstan da Tajikistan, inda kuma ya halarci taron shugabanni karo na 19 na kungiyar hadin kai ta Shanghai da taron koli karo na 5 na matakan hadin kai da amincewar juna na Asiya.

Bayan kawo karshen ziyarar, dan majalisar gudanarwar kasar kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi wa 'yan jarida bayani game da ziyarar, inda ya ce, ziyarar ta kasance ta sada zumunta da kasashe makwabtan kasar Sin ne, wadda kuma ta kai ga inganta hadin gwiwar kasashen ta fannin raya shawarar ziri daya da hanya daya. Har wa yau, ya kara da cewa, ziyarar ta yayata akidar Shanghai dake da ma'anar amincewa da juna da cin moriyar juna da zaman daidaito da juna da mutunta nau'o'in al'adu daban daban da neman ci gaba tare, baya ga haka, ziyarar ta bude wani sabon babi ta fuskar raya sabon salon huldar kasa da kasa da ma al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. A ziyarar ta kwanaki biyar, shugaba Xi Jinping ya halarci taruka sama da 30 na tsakanin bangarori biyu biyu, wadda ta inganta zumunci da amincewa da juna da kuma fahimtar juna, tare da cimma manyan nasarori. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China