Gwamnatin Najeriya tana shirin bullo da matakin rage yin bahaya a bainar jama'a
Gwamnatin Najeriya na shirin bullo da wani shiri na tallafawa marasa karfi, ta yadda za su gina tare da amfani da wuraren kewayawa, a wani mataki na rage yadda jama'a ke yin bahaya a bainar jama'a.
Ma'aikatar albarkarun ruwan kasar ta bayyana cewa, za a ba da irin wadannan tallafi ne a bangarorin yin hadin gwiwa da sassa masu zaman kansu da kamfanonin yin siminti na gida don rage kudaden gina wuraren kewayawa, ta yadda marasa karfi za su gina su kuma yi amfani da su yadda ya kamata.
Darekta mai kula da ingancin ruwa da tsaftar muhalli a ma'aikatar albarkatun ruwa ta Najeriya, Emmanuel Awe, ya shaidawa masu ruwa da tsaki yayin wata ganawa a Abuja, babbar birnin kasar cewa, sai fa an jaddada muhimmancin wannan manufa da ma canja tunanin jama'a, kafin a cimma nasarar gina karin wuraren kewayawa a sassan kasar.
Jami'in ya kuma lura da cewa, kaddamar da kamfel din "taswirar kawo karshen yin bahaya a bainar jama'a da "tsaftace Najeriya, ka yi amfani da bayan gida", na daga matakan da mahukuntan kasar ta Najeriya suka dauka na kawo karshen yin bahaya a bainar jama'a.
Awe ya ce, za a ba da tallafin ne, a wasu muhimman sassa, kamar gina kayayyakin tsaftar muhalli a wuraren taruwar jama'a, kamar makarantu, da asibitoci, a kuma damka su karkashin kulawar sassa masu zaman kansu.(Ibrahim)
Labarai masu Nasaba