Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta Kudu ya godewa mutanen da suka kada masa kuri'a
2019-05-13 10:45:44        cri
Shugaban jam'iyya mai mulkin kasar Afrika ta Kudu (ANC) Cyril Ramaphosa, ya godewa mutanen da suka kadawa jam'iyyarsa kuri'unsu, kana yayi alkawarin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar, da yaki da rashawa, da gudanar da shugabanci nagari.

Da yake jawabi a Johannesburg a lokacin wani gangami don nuna godiya ga mutanen Afrika ta Kudu wadanda suka kadawa jam'iyyarsa kuri'unsu, Cyril R amaphosa ya ce:

"Muna son godewa al'ummar kasar Afrika ta kudu da suka jajurce da nuna kwarin gwiwa wajen zaben jam'iyyar ANC. Muna son mu gode muku bisa yadda kuka nuna cewa jam'iyyar ANC ita ce kadai jam'iyyar da ta cancanci ciyar da kasarmu gaba. Kun nuna cewa ANC ita ce jam'iyyar mai nasara ga jama'armu,".

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gangamin kofa zuwa kofa, inda ya ziyarci coci-coci, da ganawa da jama'a don jin bukatunsu, inda mutanen suka bayyana damuwarsu. Jama'a sun bayyana cewa suna bukatar shugabanci nagari, da yaki da rashawa, da samar da ayyukan yi a fadin kasar. Wasu daga cikin mutanen sun yi korafin cewa ana nuna musu bambancin jinsi da rashin aikin yi.

"Za mu yi aiki tukuru don samarwa mutanen ayyukan yi. Za mu gina gidaje ga mutanenmu domin su cimma burin rayuwarsu. ANC za ta gudanar da shugabanci nagari. Za mu kawo karshen ayyukan rashawa. Za mu bunkasa tattalin arzikin kasarmu, da gayyato masu zuba jari zuwa kasarmu."(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China