Kasar Sin za ta hada kai da Afirka wajen gudanar wasu ayyuka a nahiyar Afirka
2021-12-01 09:00:00 CRI
Da yammacin ranar Litinin 29 ga wata ne, aka bude taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal, kuma shugaban kasar Sin ya halarci taron ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing na kasar Sin, tare da gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta samar wa kasashen Afirka karin alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 1, a kokarin tabbatar da manufar kungiyar Tarayyar Afirka wato AU na yi wa kaso 60 cikin 100 na al’ummomin Afirka allurar a shekarar 2022. A cikin wadannan allura, miliyan 600 daga cikinsu kasar Sin ce za ta samar da su kyauta, miliyan 400 kuma kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka masu ruwa da tsaki ne za su samar da su.
Kasar Sin za ta taimaka wa kasashen Afirka wajen aiwatar da shirye-shirye guda 10 na rage talauci da aikin gona, za ta kuma tura kwararru a fannin aikin gona 500 zuwa kasashen Afirka, tare da kafa wasu cibiyoyin zamani na gwaji da ba da horo ta fuskar fasahar aikin gona tsakanin Sin da Afirka a kasar Sin. Ban da haka kuma, kasar Sin za ta karfafawa hukumomi da kamfanoninta gwiwa da su kafa yankunan gwaji ta fuskar raya aikin gona da rage talauci a kasashen Afirka.
Har ila yau kasar Sin za ta hada kai da kasashen Afirka wajen gudanar da ayyukan guda 9, ta fuskar kiwon lafiya, rage talauci da ba da gatanci ga manoma, kara azama kan ciniki, zuba jari, yin kirkire-kirkire ta fuskar fasahar zamani, raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, kyautata kwarewar mulki, yin mu’amalar al’adu da tsaron kasa da shimfida zaman lafiya. Kamata ya yi mu tsaya tsayin daka wajen tabbatar da shawarwarin kasashe masu tasowa bisa adalci tare da aiwatar da buri da muradunmu a zahirance na bai daya
Shugaban kasar Sin ya yi imani cewa, sakamakon kokarin da kasar Sin da kasashen Afirka suke yi tare, tabbas taron zai samu cikakkiyar nasara, zai kuma hada karfin al’ummomin Sin da Afirka da yawansu ya kai biliyan 2.7 baki daya wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka baki daya.
A nasa jawabin mai masaukin bakin taron, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bayyana cewa, kasashen Afrika da kasar Sin za su kara azama a kokarin cika burinsu na samun wadata tare, domin kyautata zaman rayuwar al’ummun Afrika da Sin.Yana mai cewa, taron ya zo a daidai lokacin da ya dace bisa la’akari da sauye sauyen da ake kara samu da kuma kalubalolin dake addabar duniya wadanda suka zama tilas ga kasashen Afrika da Sin su jure ta hanyar zurfafa huldar siyasa da nuna goyon baya ga juna ta fannin tattalin arziki.
Taken taron dai shi ne “Zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika da ingiiza ci gaba mai dorewa don gina kyakkyawar makomar al’ummun Sin da Afrika a sabon zamani". (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)