Messi ya sadaukar da nasarar lashe kofin Copa America ga daukacin al’ummar Argentina da kuma Diego Maradona
2021-07-22 20:04:32 CRI
Tauraron kwallon kafar kasar Argentina da Barcelona FC Lionel Messi, ya ce ya sadaukar da nasarar da kungiyar kasar sa ta cimma, ta lashe kofin kwallon kafa na Copa America ga daukacin ‘yan kasarsa, yana mai fatan wannan nasara za ta taimaka wajen karfafa gwiwar al’ummar Argentina, a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.
Messi ya wallafa hakan ne kasa da kwana 1, bayan da Argentina ta lashe kofin na Copa America, a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa wasan karshen da suka buga da kasar Brazil ya kayatar. Ya ce “Mun san cewa muna da damar kara inganta kwarewar mu, amma a gaskiya ‘yan wasan mu sun yi namijin kokari wajen tabbatar da nasarar da muka samu, kuma hakan ya sa ni matukar alfahari, sakamakon sa’ar da na samu ta zama kyaftin din kungiyar mu a wannan karo”.
Messi ya ce "Na sadaukar da wannan nasara ga iyali na, wadanda kullum ke karfafa min gwiwar kara azama, da abokai na da nake matukar kauna, da ma sauran mutane, da daukacin al’ummar Argentina miliyan 45 da suka jurewa wahalhalu, sakamakon fama da cutar COVID-19, musamman wadanda cutar ta shafi iyalin su.
An dai buga wasan karshe na gasar kofin Copa America ne a filin wasa na Maracana dake Brazil, inda Argentina ta doke Brazil da ci 1 mai ban haushi, ta hannun dan wasan Argentina Angel Di Maria, matakin da ya kawo karshen shekaru 28 da kasar ta shafe tana jiran lashe wannan kofi.
A cewar ma’aikatar lafiyar Argentina, ya zuwa yanzu sama da ‘yan kasar sama da su miliyan 4 sun harbu da cutar COVID-19, yayin da cutar ta hallaka sama da mutum 98,000.
Don haka ne Messi, mai shekaru 34 da haihuwa, wanda aka baiwa kyautar tauraron gasar ta bana, ya ce ya sadaukar da kwallaye 4 da ya zura a raga, da tallafin zura karin wasu 5 da ya bayar yayin wannan gasa, ga tauraron kwallon kafar Argentina marigaji Diego Maradona, wanda ya rasu wasannin baya yana da shekaru 60.
Ya ce "Wannan nasara ce ta daukacin ‘yan Argentina, da kuma Diego, wanda ko shakka babu ya taimaka mana daga inda yake” Messi ya kuma karfafawa ‘yan wasan kwallon kafar kasarsa gwiwar ci gaba da kwazon su, a fannin aiwatar da matakan dakile yaduwar wannan annoba.
Ya ce "Domin ci gaba da shagulgula, dole mu kare kawunan mu. Kar mu manta muna da tafiya mai nisa kafin komai ya koma daidai. Ina fatan za mu yi amfani da damar mu ta wannan murna da muke yi, wajen karfafa ayyukan mu na yaki da wannan annoba tare."
Kafin wannan, a ranar Lahadi, dan wasan Brazil Neymar, ya wallafa sako a shafin sa na yanar gizo, inda ya bayyana goyon bayansa ga sakon tsohon abokin wasan sa a Barcelona, kuma Aminin sa wato Messi.
A sakon na sa, Neymar wanda a yanzu ke takawa PSG leda ya ce "Rashin nasara yana min ciwo. Abu ne da har yanzu ban saba da shi ba. A jiya, duk da mun yi rashin nasara, na je domin rungumar dan wasa mafi kwarewa da na taba haduwa da shi: Aboki na ne, kuma dan uwa na. Ina cikin damuwa, amma na fada masa cewa, "Jarumi, ka samu nasara a kan mu."
"Ina cikin damuwar rashin nasara. Amma wannan gwarzo ne mai kwarewa! Ina matukar girmama irin gudummawar da ka bayar ga kwallon kafa, musamman gare ni. Bana son rashin nasara. Amma ina fatan za ka ji dadin wannan nasara, kwallon kafa ta jima tana jiranka."