logo

HAUSA

Zuwa da kai ya fi sako

2021-06-22 14:41:47 CRI

Zuwa da kai ya fi sako_fororder_A

Batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, musamman ma ’yancin bin addini, abubuwa ne dake ci gaba da jan hankalin duniya, musamman al’ummar musulmi, inda suke ganin baiken kasar Sin, sanadiyyar karairayi da jita-jitar da wasu dake da wata mummunar manufa ke yadawa don cimma wasu bakutunsu.

Hausawa kan ce zuwa da kai ya fi sako, haka kuma gani ya kori ji. Duk wanda yake jin labaran da ake yadawa dangane da jihar, zai yi fargabar zuwa tare da tunanin irin mummunan yanayin da ita da ma al’umarta ke ciki. Sai dai  maimakon ganin tashin hankali, sai na tarar da zaman lafiya, maimakon ganin koma baya, sai na tarar da dimbin ayyukan ci gaba da ababen more rayuwa, maimakon ganin mutane cikin kunci, sai na tarar da su cikin walwala, maimakon ganin mabiya addini cikin tsoro da fargaba, sai na tarar da su cikin kwanciyar hankali kamar kowanne dan kasa, maimakon ganin matsanancin talauci, sai na tarar da arziki da wadata. Hakika idona ya gane min sabanin tunanina da kuma irin labaran karya da ake yadawa.

Zuwa da kai ya fi sako_fororder_B

Wuri na farko da na yada zango a jihar Xinjiang shi ne kwaleji ko jami’ar nazarin addinin Musulunci, inda kaso 70 na darussan wannan kwaleji ya mayar da hankali kan koyar da ka’idoji da dokokin addinin musulunci, baya ga uwa uba karatun al’Qur’ani mai tsarki da tafsirinsa. Duk wanda ya bar gida, aka ce  gida ya bar shi. Sai dai wannan karin magana ce da har kullum kasar Sin ba ta yin kasa a gwiwa wajen ganin al’ummarta ba su bar gida ba, bare gidan ya bar su. Abun nufi, tana tsayawa haikan wajen kiyaye al’adunta na gargajiya tare da tabbatar da cewa kowanne dan kasa ya fahimta, don haka ne sauran kaso 30 na darussan kwalejin suka kunshi nazarin dokoki da al’adun kasar Sin da kuma daidaitaccen harshen Sinanci bisa la’akari da cewa, mutanen jihar na da irin nasu harshe. Wannan kuma zai ba su damar fahimtar sauran ’yan uwansu Sinawa tare da fahimtar yanayin harkokin kasa. Kamar yadda kowanne kwaleji ko jami’a take, dalibai da kansu ke neman gurbin karatu sannna su rubuta jarabbawar tantancewa kafin su samu gurbin karatu. Wannan na nuna cewa, bisa radin kansu daliban ke karatu a wannan kwaleji da ya kunshi masallaci da dakunan kwana da ajujuwa da dakin cin abinci da sauransu.

Abun tambaya a nan shi ne, shin me ya sa gwamnati za ta gina irin wannan kwaleji domin koyar da addini idan har tana hana bin addinin? Me ya sa za ta rika ba daliban wannan kwaleji tallafin karatu da kyautata walwalarsu da muhallin karatun idan har so take ta dakile ’yancin bin addini da kuma musulmai? Har kullum na kan yi mammaki idan na ziyarci yankunan musulmin kasar Sin domin yadda nake tarar da su suna gudanar da ibada kamar yadda ya kamata: ba tsoro ba tsangwana. Kasar Sin ba kasa ce ta musuluci ba, amma kuma kundin tsarin mulkinta ya bada dama ko ’yanci ga kowanne dan kasa ya zabi addinin da yake so, kana gwamnatin na kokarin ganin al’ummarta sun rayu cikin jin dadi da walwala ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.

Zuwa da kai ya fi sako_fororder_C

Yadda masu tsattsauran ra’ayi ke adawa da zaman lafiya a duniya, abu ne da bai kamata a nuna masa halin ko in kula ba. Hakika kasar Sin kasa ce mai tsauri da ba ta daukar wargi, inda kamar ko da yaushe, ta dauki tsauraran matakan yaki da ta’addancin da ya kunno kai a jihar Xinjiang. Ai da zafi-zafi a kan daki karfe! Abun da kafafen yammacin duniya ba sa sanarwa shi ne, ayyukan ta’addancin da aka fuskanta a baya a jihar Xinjiang, wadanda suka haifar da asara dukiya da rayuka. Kuma bisa tsauraran matakan kasar, ta yi nasarar dakile su tare da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba. Kana tana ci gaba da daukar matakai domin ganin ba a samu makamancin lamarin ba a nan gaba. Yin wasarairai da harkokin da suka shafi tsaro ko zaman lafiya, su ne suke kai wa matsayin da lamarin zai gagari kundila. Idan a ce dukkan kasashe na daukar irin wadannan, da zancen ta’addanci ko rikicin kabilanci da rashin tsaro ya zama tarihi a kasashen duniya, kamar yadda ya zama a kasar Sin.

Yayin da rikice-rikice da tashe-tashen hankula suka zama ruwan dare a duniya, Kasar Sin na cikin jerin  kasashen dake more zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba cikin sauri a duniya. A tunanina, ci gaba da kuma karbuwar da Sin take samu tsakanin kasashen duniya cikin kankanin lokaci ne suke tsoratar da masu yada jita-jita, inda suke fakewa da ’yancin addini ko hakkin dan Adam domin bata mata suna, bayan sam lamarin ba haka yake ba a zahiri. (Fa’iza Mustapha)