logo

HAUSA

Kasar Sin za ta taimakawa kasashen Afirka ba tare da tangarda ba wajen neman bunkasa Afirka

2021-03-10 09:00:00 CRI

A ranar Lahadin da ta gabata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kira taron manema labarai, yayin zama na hudu na taron majalisar wakilan jama’ar kasar karo na 13 dake gudana yanzu haka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Kasar Sin za ta taimakawa kasashen Afirka ba tare da tangarda ba wajen neman bunkasa Afirka_fororder_20210310世界21008-hoto2

Yayin taron, Wang ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da ra’ayi na kashin kai da wasu kasashe ke nunawa wajen mallakar riga-kafin COVID-19, da daina neman siyasantar da hadin gwiwar kasashen duniya na samar da riga kafin.

Haka kuma, kasar Sin tana fatan kasashen duniya, za su yi kokarin samar da riga-kafin ga kasashe mabukata, musamman kasashe masu tasowa, ta haka ne al’ummar duniya za ta samu riga kafin cikin sauki har ma ya taimakawa duniya baki daya.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samar tare da ci gaba da samar da tallafin riga-kafin COVID-19 ga kasashe masu tasowa kimanin 69, baya ga kokarin da take yi na fitar da riga-kafin zuwa kasashe kimanin 43.

Wang Yi ya kuma karyata labaran boge da wasu suke kitsawa game da wai, ana kisan kare dangi a yankin Xinjiang na kasar Sin, da tsoma baki a harkokin HK, duk don neman bata sunan kasar Sin. Kasar Sin a cewar Wang yi, za ta inganta tsarin zabe a yankin na HK, da aiwatar da ka’idar barin ‘yan kishin kasa su rika gudanar da harkokin zabe a yankin.

Kasar Sin za ta taimakawa kasashen Afirka ba tare da tangarda ba wajen neman bunkasa Afirka_fororder_20210310世界21008-hoto3

Kan batun nahiyar Afirka kuwa, Wang Yi ya ce, kasarsa ta taimakawa kasashen Afirka a fannin yaki da cutar COVID-10, gami da farfado da tattalin azrkinsu, wanda hakan abu ne mai muhimmanci ga hadin gwiwar sassan biyu wato Sin da Afirka.

Ya ce, a taron musamman na hadin gwiwar Sin da Afirka game da yaki da COVID-19, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da sabbin matakan tallafawa nahiyar Afirka. Ya zuwa yanzu, Sin ta tura kayayyakin yaki da cutar zuwa kasashen Afirka kusan 15, ta kuma tura alluran riga kafi ga kasashen nahiyar 35 da AU. Haka kuma, kasar Sin ta taimaka wajen gina hedkwatar Africa CDC, da gaggauta hadin gwiwa wasu asibitoci Sin da Afirka 30.

A bana ne, dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) yake cika shekaru 20 da kafuwa, dandalin dake zama abin koyi a hadin gwiwar Sin da Afirka. Kuma a bana ne za a gudanar da taron dandalin a kasar Senegal. Wang Yi ya tabo bututuwa da dama da suka shafi harkokin diflomasiya, da tsaro, tattalin arziki da wasu muhimman fannoni dake shafar ci gaban kasar Sin da sauran kasashen duniya. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)