"Hutong" na birnin Beijing
2021-02-26 20:05:14 CRI
Ma'anar kalmar "Hutong" ita ce farfajiya, ko kuma karamar hanya. Tsarin "Hutong" shi ne wata karamar hanya, sa'an nan a gefunan hanyar akwai gidaje na jama'a. Ma iya cewa, "Hutong" ungwanni ne na gargajiya da mutanen Beijing suke zama a ciki. Yaya wadannan ungwanni suke a wannan zamanin da muke ciki? Bari mu bi Bello Wang da Saminu Alhassan, mu shiga cikin ungwannin "Hutong" don samun amsa. (Bello Wang)