logo

HAUSA

Kara yin ma'amala da mutane zai rage matsalar mantuwar tsoffafi

2021-01-10 10:44:46 CRI

Kara yin ma'amala da mutane zai rage matsalar mantuwar tsoffafi_fororder_src=http___n.sinaimg.cn_translate_600_w1920h1080_20190209_WQJl-hsqyiwu6682237&refer=http___n.sinaimg

Masu nazari daga kasar Birtaniya sun kaddamar da bayanin nazari a kwanan baya, inda suka yi nuni da cewa, tsoffafin da suke mu’amala da mutane kullum ba su fuskantar babbar barazanar da gamuwa da matsalar mantuwa, in an kwatanta su da sauran takwarorinsu.

Masu nazarin daga jami’ar London ta kasar Birtaniya sun tantance bayanan da suka shafi zaman rayuwar mutane fiye da dubu 10 da kuma lafiyarsu. Kana kuma daga shekarar 1985 zuwa shekarar 2013, sau da dama, masu nazarin sun yi bincike da jarrabawa kan yadda wadannan mutane suka yi mu’amala da mutane da kuma kwarewarsu ta adanawa da koyon muhimman abubuwa. An kuma sabunta bayanan lafiyar har zuwa shekarar 2017. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, a lokacin da shekarunsu suka kai 60 da haihuwa, idan an kwatanta wadanda suka sadu da abokansu a ko wace rana, mutanen da suka sadu da abokai cikin ‘yan watanni da dama sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar mantuwa da kaso 12 cikin 100. Har ila yau kuma, idan mutane sun kara yin mu’amala da al’umma a yayin da shekarunsu suka kai 50 da kuma 70 da haihuwa, to, ana zaton cewa, za su rage barazanar gamuwa da matsalar mantuwa. Amma duk da haka raguwar barazanar ba ta kai ta lokacin da shekarunsu suka kai 60 ba. Masu nazarin suna ganin cewa, kara yin mu’amala da al’umma a ko wadanne shekaru yana taimakawa wajen rage barazanar gamuwa da matsalar mantuwa.

Rahotanni na nuna cewa, wasu nazarce-nazarce da aka gudanar a baya sun shaida mana cewa, akwai wata alaka tsakanin batun kara yin mu’amala da al’umma da kuma raguwar barazanar gamuwa da matsalar mantuwa. Amma ba a samu isassun bayanan masu ruwa da tsaki ba, kuma ba a dauki isasshen lokaci wajen gudanar da nazari ba. Akwai yiwuwar cewa, watakila mutane sun rage yin mu’amala da al’umma ne saboda kwarewarsu ta adanawa da koyon muhimman abubuwa ta samu koma baya. Bayanan da masu nazarin na kasar Birtaniya suka dauki tsawon shekaru suna samu sun kasance abun shaida dangane da yadda kara yin mu’amala da al’umma yake amfani a fannin raguwar barazanar gamuwa da matsalar mantuwa.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, yin mu’amala da al’umma yana kyautata kwarewar mutane ta fannonin adana muhimman abubuwa, yin magana da dai sauransu. Yana taiamaka wa kwakwalwar mutane wajen kara daidaita matsalar tsufa. Sa’an nan kuma saduwa da abokai yana wa mutane damar motsa jiki. Dukkansu suna amfani ga tsoffafi wajen rage barazanar gamuwa da matsalar mantuwa. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan