Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:16:04    
An fara aikin shimfida hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a tsakanin birnin Beijing da Shanghai na kasar Sin

cri

A cikin shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta sami kyakkyawan sakamako wajen binciken fasahar gina hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri. Malam Lu Chunfang, mataimakin ministan sufurin jirgin kasa na Sin ya bayyana cewa, gina hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a tsakanin Beijing da Shanghai zai kyautata tsarin fasahar gina hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a kasar Sin. Ya kara da cewa, "yin amfani da kyakkyawar fasahar da aka riga aka samu wajen gina hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a tsakanin Beijing da Shanghai, zai daga matsayin kasar Sin na zamanintar da hanyoyin jirgin kasa. Haka kuma zai ba da taimako wajen bunkasa sana'o'in kera injuna da kayayyaki masu aiki da wutar lantarki da na samar da danyun kayayyaki da labaru da sauransu, ka zalika zai inganta kwarewar kasar Sin wajen yin kirkire-kirkire cikin dogara da karfin kanta."

Yanzu, dukkan tsawon hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri da aka riga aka gina ya wuce kilomita dubu 10 a duniya, haka kuma tsawon irin wannan hanyar da ake aikin gina ta shi ma ya wuce kilomita dubu 10 a duniya.(Halilu)


1 2 3 4