Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:16:04    
An fara aikin shimfida hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a tsakanin birnin Beijing da Shanghai na kasar Sin

cri

Ran 18 ga watan Afrilu da ya wuce, an kaddamar da aikin shimfida hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri wadda za ta hada manyan biranen Beijing da Shanghai na kasar Sin. A karkashin shirinta, kasar Sin da kanta za ta kammala dukan aikin gina wannan hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a cikin shekaru biyar, hanyar hanya ce mafi tsawo da kyau da za a gina a duniya a lokaci guda. Bayan da aka kammala aikin gina hanyar, yawan mutanen da za a yi jigila a tsakanin birnin Beijing da Shanghai zai kai miliyan 160 a ko wace shekara, lokacin tafiya ma zai ragu daga awoyi 10 zuwa awoyi 5.

Malam Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya halarci bikin kaddamar da aikin shimfida wannan hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri da aka shirya a birnin Beijing a wannan rana, kuma ya sanar da cewa, an fara aikin shimfida hanyar. Ya ce, "an fara aikin shimfida dukan tsawon hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri da za ta hada birnin Beijing da Shanghai. "


1 2 3 4