Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:16:04    
An fara aikin shimfida hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri a tsakanin birnin Beijing da Shanghai na kasar Sin

cri

Dukan tsawon hanyar ya kai kilomita 1318, yawan kudin da za a kashe wajen gina ta zai tashi kimanin kudin Sin Yuan biliyan 220, wannan makudan kudi ya yi yawa sosai har ba a taba ganin irinsa ba tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Bisa shirin da aka tsara, jirgin kasa mai tafiya da sauri zai yi tafiyar kilomita 350 a cikin awa daya. Wannan hanyar za ta hada manyan birane 3 kamar Beijing da Tianjin da Shanghai da kuma jihohi 4 kamar Hebei da Shandong da Anhui da Jiangsu. Malam Zhang Dejiang, mataimakin firayim ministan kasar Sin ya bayyana cewa, gina wannan hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri yana da muhimmanci sosai ga wadannan manyan birane da jihohi wadanda ke bunkasa harkokin tattalin arzikinsu cikin sauri. Ya kara da cewa, "shimfida hanyar jirgin kasa mai tafiya da sauri ta zamani a yankin inda ake ta kara bukatar jigilar mutane da kayayyaki masu yawa, yana da muhimmanci sosai ga sassauta hali mai tsanani da ake ciki dangane da zirga-zirgar jiragen kasa, da kyautata tsarin masana'antu na kasar Sin, da gaggauta bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma cikin sauri kuma da kyau."


1 2 3 4