Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani

• Gidan rediyon kasar Sin ya taya murnar ranar cikon shekaru 65 da kafuwarsa
More>>
• An taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin
Yau da shekaru 65 da suka wuce, wata wayar rediyo ta fito daga wani kogon da ke arewa maso yamma na kasar Sin. Wannan ne karo na farko da gidan rediyo na Xin Hua da ke garin Yan'an ya watsa shirinsa da harshen Japan. Gidan rediyo na Xin Hua da ke garin Yan'an, tsohon suna ne na gidan rediyon kasar Sin na yanzu
Bayanin ranar taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin
Saurari
• Bari mu raya wani kafar watsa labaru ta zamani tare
Jiya wato ran 3 ga wata, an yi bikin taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin da yake kasancewa tare da ku a kowane lokaci. Lokacin da aka kafa shi a wani kogon dutse a garin Yan'an da ke arewa maso yammacin kasar Sin yau da shekaru 65 da suka wuce, ya watsa labaru ga masu sauraro da harshe daya, wato harshen Japan kawai. Amma, yanzu ba ma kawai yana watsa labarun kasar Sin da na duniya da harsuna 43 ba, har ma yana tsara da watsa labaru ta rediyo da na talibijin da shafin internet da jarida, wato ya riga ya zama wata kafar watsa labaru ta zamani. Yanzu, a cikin shirinmu, za mu gabatar da shugaba Wang Gennian na gidan rediyon kasar Sin a cikin dakinmu na daukar murya
• Bayani kan tarihin Rediyo Kasar Sin don murnar cikon shekaru 65 da kafa shi
Ranar 3 ga watan Disamba rana ce ta cikon shekaru 65 da kafa gidan rediyo kasar Sin wato CRI. Yau da shekaru 65 da suka wuce, wayar gidan rediyonmu maras karfi ta tashi daga Yan'an, wani karamin gari da ke arewa maso yammacin kasar Sin, daga nan dai rediyonmu ya soma watsa shirye-shirye cikin harsuna da yawansu kullum ke kara karuwa sannu a hankali, muryar rediyonmu ya kara yaduwa zuwa wurare daban daban, sa'an nan kuma aminai da suka kulla abuta da rediyonmu kullum sai kara karuwa suke yi
• Sakonnin taya murna daga masu sauraro(3)
A ran 3 ga watan Disamba na shekara ta 1941 ne, aka kafa gidan rediyon kasar Sin, wato CRI, wato daidai a ran 3 ga watan nan da muke ciki ke nan, CRI ya cika shekaru 65 da kafuwa. A kwanakin baya, bi da bi ne masu sauraronmu suka rubuto mana wasiku, inda suka taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa.
• Sakonnin taya murna daga masu sauraro(2)
Don taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa, malam Hamza M Djibo, wanda ya fito daga birnin Niyame jamhuriyar Nijer, ya rubuto mana cewa, shekaru 65 na CRI shekaru ne da masu sauraro suka karu da su sosai musamman ga su jin harshen Hausa
• Wani mai sauraronmu daga jihar Kano ta kasar Nijeriya Shuaibu ya taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar CRI
Ya ce, Ina tayaku murnar cika shekaru 65 da bude wannan gidan rediyo.Allah ya ja zamani Amin a madadin Mustapha Tanko Abdullahi. Wani mai sauraronmu Abba Muhammad Nuhu shi ma ya zo daga jihar Kano ya aiko da Email cewa, Allah ya bar CRI! Allah ya bar ma'aikatanCRI!! Allah ya bar jamaar kasarSin!!!'
• Bayan haka, wani kulab na masu sauraron gidan rediyon kasar Sin wato JEKADAFARI YOUTH RADIO LISTENERS ASSOCIATION ya rubuta wata wasika gare mu
Shugaban kulab MUSA ADAM ABUBAKAR da sakatarensa SA'AD IBRAHIM GOMBE da kuma mataimakin shugaban kulab din MOH'D YERO (TEA-MAKER) sun taya murna musamman ga cikon shekaru 65 na CRI
• Wani mai sauraronmu da ya zo daga jihar Nasarawa ta kasar Nijeriya Sanusi Isah Dankaba ya rubuta wani Emial musamman domin taya murnar cikon shekaru 65 na kafuwar CRI
Ya ce haka, 'Radiyon kasar sin wani muhimmin tashar rediyo ce wadda take watsa shirye-shiryen ta a duk fadin duniya a cikin harsuna sama da arbain. akwana atashi wata rana jariri ango ne,yau gashi allah yanuna mana gidan rediyon kasar ta cika shekaru sittin da biyar dakafawa wannan tasha mai farin jini.
• Sakonnin taya murna daga masu sauraro
Don taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa, shugaban kungiyar masu sauraron CRI ta Gombawa, malam Mohammed Idi Gargajiga ya rubuto mana cewa, da farko, ina sanar da ku cewa, a madadin dukkan masu sauraro na kungiyar COMBAWA CRI LISTENERS CLUB mai mambobi 1612 kuma bisa matsayina na shugaban club, muna taya CRI murnar cika shekaru 65 da kafuwa.