Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-03 17:31:50    
Gidan rediyon kasar Sin ya taya murnar ranar cikon shekaru 65 da kafuwarsa

cri

Ran 3 ga watan Disamba rana ce ta cikon shekaru 65 da kasar Sin ta kafa sha'anin watsa labaru ga kasashen waje da kuma gidan rediyon kasar Sin. Yau an yi kasaitaccen babban taron tunawa a nan Beijing.

Zaunannen wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Li Changchun ya aika da wasikar taya murna, inda ya taya wa dukan ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin murna da kuma yin musu jaje. Ya kuma yi fatan cewa, gidan rediyon kasar Sin zai kara bayyana ra'ayin da kasar Sin ke tsayawa a kai, wato nacewa ga samun bunkasuwa cikin lumana da ingiza raya duniya mai jituwa, zai kuma gaggauta kafa tsarin watsa labaru na duniya na zamani, ta haka zai kara ba da gudummawa wajen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kuma aikin raya kasa ta zamani ta fuskar gurguzu da kasar Sin take yi.

A cikin jawabin da ya yi, ministan ba da labaru na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Liu Yunshan ya jaddada cewa, dole ne a nace ga dacewa da halin da kasar Sin ke ciki wajen samun ci gaba, da biyan bukatar da mutanen kasashen waje suke gabatarwa kan kasar Sin, da kuma dacewa da al'adar da mutanen kasashen waje su kan saba bi, ta haka gidan rediyon kasar Sin zai kara kyautata shirye-shiryensa.

Shugaban babbar hukumar kula da watsa labaru da sinima da telibijin ta kasar Sin Wang Taihua da kuma shugaban gidan rediyon kasar Sin Wang Gengnian su ma sun yi jawabai a gun wannan babban taro.

Shugabanni Mwai Kibaki na kasar Kenya da Jacque Chirac na kasar Faransa da Durao Barroso na kwamitin Kungiyar Tarayyar Turai da shugabannin wasu kasashen waje sun aika da sakon taya murna ga gidan rediyon kasar Sin.(Tasallah)