Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-20 17:11:54    
Sakonnin taya murna daga masu sauraro(3)

cri

A ran 3 ga watan Disamba na shekara ta 1941 ne, aka kafa gidan rediyon kasar Sin, wato CRI, wato daidai a ran 3 ga watan nan da muke ciki ke nan, CRI ya cika shekaru 65 da kafuwa. A kwanakin baya, bi da bi ne masu sauraronmu suka rubuto mana wasiku, inda suka taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa.

Don taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa, malam Sani Mohammed daga Musa Umar Street Mando, Kaduna, Nijeriya ya rubuto mana cewa, ina matukar taya daukacin mutanen kasar Sin, da ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin da kuma shugaban babbar hukumar watsa labaru da Sinima da Talabijin ta kasar Sin, wato Wang Taihua, da ma shi kansa, Wang Gengnian, shugaban rediyon kasar Sin, a bikin cika shekaru 65 da kasar Sin ta kafa sha'anin watsa labaru ga kasashen waje da kuma rediyon kasar Sin. Ina muku murna da kuma farin cikin cimma wannan babban matsayi na shekaru aru-aru da gabatarwa da watsa shirye-shirye a duniya.

Hasali ma dai, sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya wuce gagara misali, ya zama ya yi wa tsara fintinkau.

Ina so in yi amfani da wannan dama, in kara nuna jin dadinmu da shirye-shiryenku musamman ma ta hanyar na'urar internet. Shafinku shi ya fi na ko wane gidan rediyo a duniyar nan kayatarwa da ilmantarwa. Gidan rediyon kasar Sin da ma kuma musamman shafinku na internet wata makaranta ce wadda ake samun ilmi ingantacce kuma kyauta.

A karshe, ina bakin cikin rashin samun damar jin shirye-shiryenku ta rediyo kai tsaye, sabo da yanayin inda nake zama da kuma irin akwatin rediyon da nake amfani da shi. Shi ya sa nake dogara ga shafinku na internet domin karanta shirye-shiryenku.

Ina kara mika godiya ta musamman daga ni da sauran masu sauraronku a kullum wadanda ba su samu damar isar da sakonsu a gare ku ba.

Sai kuma malam Ibrahim Muhammad Zaria, mazaunin Garki Abuja Nijeriya, ya rubuto mana cewa, wannan wasikar sada zumunci ce zuwa gare ku baki daya, da fatan kuna lafiya kamar yadda nake tare da iyalina a nan Abuja, Nijeriya.

Bugu da kari, wannan wasikar taya ku murnar cika shekaru 65 ne da kafuwa. Hakika, gidan Rediyo na kasar Sin ya cancanci yabo, musamman saboda namijin kokari da kuke yi tun ranar 3 ga Disambar 1941 har zuwa yau.

Da fatan wannan namijin kokari naku zai zama hanyar dada cin gaban CRI da kuma kasar Sin baki daya.

Bayan haka, sakon da malam Abdullahi Garba Baji, shugaban Mobaji Radio Club International, ya aiko mana, na yin nuni da cewa, mu 'yan kungiyar Mobaji Radio Club International, muna taya ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin murnar cika shekaru 65 da fara shirye-shiryen CRI, muna jin dadin shirye-shiryenku na Hausa.

Sai kuma malam Abba Mohammed Nuhu daga birnin Kano, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, bayan miliyoyin gaisuwa mai yawa, dalilin wannan wasika shi ne, don in taya ku murnar cika shekaru 65 da kafuwa. Ina yi muku fatan alheri, kwarin gwiwa, koshin lafiya a ko da yaushe. Allah ya bar CRI! Allah ya bar ma'aikatan CRI!! Allah ya bar jama'ar kasar Sin!!!

Bayan haka, malam Mustapha Tanko Abdullahi daga Garangamawa D.Sambo, Kano, Nijeriya, ya ce, ina taya ku murnar cika shekaru 65 da bude wannan gidan rediyo, Allah ya ja zamani, Amin.

A madadin dukan ma'aikatan CRI, musamman ma ma'aikatan sashen Hausa, ina mika godiyarmu ga wadannan aminai masu sauraronmu, sabo da goyon bayan da kuka ba mu, wanda ya sa mana kaimi, kuma ya taimaka mana wajen kyautata shirye-shiryenmu. Nan gaba za mu kara yin kokari, don jin dadinku.