Ra’ayin Excellency kan kasar Sin


Ra’ayin Alhajji game da kasar Sin shi ne dukkan mutumin da ya zo daga kasashe masu tasowa, ya zama wajibi ya yi kokari ya ziyarci kasar Sin, ba don kome ba, don yarda irin ci gaba da ta samu, a cikin dan kadan lokaci kayadadde, kuma ya kamata ya zama abin koyi ne gare mu, kuma mu tabbatar da cewa irin hanyoyin da kasar Sin take bi don cimma wannan nasara, ya zama lalle ne mu kasance masu koyi kuma mun tabbatar da cewa al’ummarmu su ma, za su sami irin jin dadi wadanda shugabanni da gwamnatin China suke kokarin aiwatarwa wajen tabbatar da jin dadin al’ummarsu, mu ma ya zama wajibi ne mu tabbatar da cewa, mun karkata ga irin tafarki wanda zai tabbatar da jin dadin al’umma da kwanciyar lafiya da tsaro a kasar.