Yadda za a kara hada kai ta fuskar al’adu tsakanin kasashen biyu
Harkar al’adu na gargajiya, kamar yadda ka sani, kasar Sin wadda ke da dadaddiya, kuma in an duba wayewar kanta, za a ga suka fara kawo wasu abubuwa ga sauran al’ummomin duniya tun shekaru dubu da suka wuce, sabo da suna da karfafun al’adu, wandada har yanzu suke amfani da su, to a nan ana gani, ya yi kyau, ni zuwana, in yi nazari a kan abin da ya faru a kasar nan, sa’an nan a nemi mu yi koyi da yadda kasar Sin ta iya hada tattalin arzikin kasarta da ci gaban kasarta, ta auren da su da al’adunta na gargajiya, wanda aka samu kwaran ci gaban, sabo da haka, al’adun gargajiya su kan taimaka ba kadan ba, wajen taimakawa kyakkyawa zamantakewar al’umma, da tattalin arzikin kasar.
Mu’amala ta cinikayya tsakanin Nijeriya da China
Wannan abu wanda ke da karfi, a halin yanzu, mu Nijeriya muke da bukatar kasar Sin shigo mana ta sigar, yadda za su taimakawa masana’antunmu da al’ummarmu, ba wai su zo ne, don su yi ciniki, su sami abin duniya, su tafi, a’a sun dauko dukiyarsu, su kawo Nijeriya su sami harkar hadin gwiwa tsakaninsu da mutanen Nijeriya, mu ma mun amfana, su ma sun amfana, jama’armu sun sami aiki, kuma an sami ci gaba gaba daya.
Ra’ayin Alhajji kan Taron baje-koli na Shanghai
Wannan ina kira wa dukkan ‘yan kasuwanni namu manya-manya da kuma kamfanoni manya-manya na Nijeriya da suka zo wannan kasar China, don halartar taron baje-koli na Shanghai, don za su iya ganin irin abubuwan da suke faruwa a kasar Sin, da kuma kamfanonin da za su iya hulda da su, da wadanda za su zuwa Nijeriya, su je su kafa masana’antu, ko dai da kansu ko kuma hadin gwiwa da Nijeriya, to, wannan kasuwa ce za ta ba da dama, dukkanin ‘yan kasuwa na kirki, ya zo ya gani halin wannan taron baje-koli, wanda za a gani, zai ba da dama.
Nijeriya za ta nuna abubuwan da take da shi, na dukiyoyin kasarta, wanda China take bukatarta, kamar kayan amfanin gona, da ma’adinai, da mai da dai dukkan abubuwan da za a iya samun riba ta hulda kansu da China, mun ma, za mu nuna taimako da gwamnati take bayarwa, ga dukkanin mutanen da suke da sha’awa, su zo, su yi harkar cinikayya, gwamntin Nijeriya za ta taimake gare su, kuma mu taimako wajen hutun haraji.