Rawar da Nijeriya ke takawa a duniya


Nijeriya ta riga ta yi zara da sauran dukkan kasashen Afrika, na taimakawa da kawo zaman lafiya a ciki da wajen Afrika, na san Nijeriya tun 1960, muka samu mulkin kanmu, muka fara aika da sojojinmu, wajen taimakawa kiyaye zaman lafiya a M.D.D a kasar Kongo, kana, har kawo yau, ko wane lokaci, ana gane akwai sojojin Nijeriya da ‘yan sanda a kasashen duniya, inda ake samun rigingimu, wanda Nijeriya ta tura sojoji da ‘yan sanda, don su taimaka su sami zaman lafiya, sabo da haka Nijeriya ta yi rawar gani fiye da dukkanin wata kasa a Afrika a yau wajen harkar kyautata zaman lafiyar mutane a ko ina ake samun rigingimu a duniya.