{aura da sake matsuguni wani abu ne mai wuya bisa al’adun Sinawa. A zamanin da tilas ne ka duba kalanda domin za~in lokacin da ya dace. Lokaci mafi kyau da ya dace da }aura shi ne kafin tsakiyar rana kuma kafin fa]uwarta, domin }aura da daddare ba abu ne mai kyau ba. A lokacin }aura tilas ne a yi kalamai masu da]i, kuma kada wani daga cikin iyali ya yi kuka ko hushi, kada kuma su doki yaransu, kuma kada su yi barci a ranar ko yin barci a sabon gidan, in ba haka ba, za su kamu da ciwo a nan gaba. Da dare, mutane kan dafa abinci, da kuma cin abincin tare da iyalansu da zummar inganta ha]in kan iyalan da kuma samun fatan alheri da wadata. Amma a halin yanzu, mutane ba safai su kan mai da hankali kan wa]annan al'adun gargajiya ba, har ma wasu ka]an sun san su. Duk da haka, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne neman wani kamfanin ]aukar kaya. Ban da wannan kuma, mutane kan gayyaci abokan aikinsu da abokansu cin abinci tare da zummar murnar canja gida.