Daga cikin harsunan da ake amfani da su a halin yanzu a }asashe daban daban, Sinanci harshe ne ]aya kawai da babu harufa cikin kalmominsa. Game da asalin kalmomin Sinanci, akwai tatsuniyoyi da dama. An ce, a zamanin gargajiya, akwai wani mutum mai suna 仓颉(cānɡ jié), wanda ya sami zummar }ir}iro kalmomin Sinanci bisa sawun }afafuwan tsuntsaye a cikin ta~o, sabo da haka, ya }ir}iro ainihin kalmomin Sinanci.
Daga baya, a kabarin da ke dab da kogin Lingyang na garin Ju da ke lardin Shandong na }asar Sin, masanan kayan tarihi na sabuwar }asar Sin sun gano ]imbin kayayyakin tarihi, kuma sun gano zane-zanen kalmomi a kan wasu tukwane. Bisa nazarin da aka yi, an ce, kalmomin na da tsawon tarihi fiye da shekaru 4500, kuma sun kasance farkon kalmomin Sinanci.
Don taimaka wa jama’a wajen karanta kalmomin Sinanci daidai, a shekarar 1958, a hukunce ne gwamnatin }asar Sin ta }addamar da shirin Pinyin na harshen Sinanci, shirin ya yi amfani da harufan Latin wajen rubuta kalmomin Sinanci bisa lafazinsu.
Shirin Pinyin na harshen Sinanci tsarin wasu alamu ne da ke nuna mana lafazin Sinanci, kuma ya kasu cikin kashi biyu, wato akwai wasula 21 da kuma ba}a}e 39.