量词在名词的前面
Wata siga ta daban ta Sinanci ita ce a kan yi amfani da ma’auni a gaban suna, kuma an fi yin amfani da 个(gè).
Ba mu ce mutum ]aya ba, sai mutum 个(gè) ]aya. 一个人 (yí gè rén), wato mutum ]aya, 两个人 (liǎng gè rén), wato mutane biyu.
Wani ma’auni na daban shi ne 条(tiáo), wanda a kan yi amfani da shi wajen bayyana dogon abu siriri. Sabo da haka, mu kan ce, hanya 条 ]aya. 一条路 (yì tiáo lù), wato wata hanya, 两条路 (liǎng tiáo lù), hanyoyi biyu.
Ban da wannan kuma, a kan yi amfani da kamla 头 (tóu) don siffanta dabbobi. Ma'anar 头 (tóu) ita ce kai. Don haka, mu kan cewa, shanu 头 uku, 三头牛 (sān tóu niú), wato shanu uku.