Darasi na 31 Halin Musamman na Sinanci

 Hira da CRI
 
  • A game da Pinyin, akwai amo hu]u a cikin Pinyin na Sinanci, wato amo na farko da na biyu da tashin amo da kuma saukar amo. Wato, Pinyin ]aya na da amo hu]u, wa]anda kuma ke da ma’ana daban daban. Alal misali, mā (妈), má (麻), mǎ (马), mà(骂).
    Kuma dole ne mu yi nuni da cewa, amo daban, ma’ana daban. Misali 妈 (mā) na nufin mama.A yayin da马(mǎ), amo na uku, na nufin “doki”.
  • Wata siga ta daban ta Sinanci ita ce a kan yi amfani da ma’auni a gaban suna, kuma an fi yin amfani da 个(gè).
    Ba mu ce mutum ]aya ba, sai mutum 个(gè) ]aya. 一个人 (yí gè rén), wato mutum ]aya, 两个人 (liǎng gè rén), wato mutane biyu.
    Wani ma’auni na daban shi ne 条(tiáo), wanda a kan yi amfani da shi wajen bayyana dogon abu siriri. Sabo da haka, mu kan ce, hanya 条 ]aya. 一条路 (yì tiáo lù), wato wata hanya, 两条路 (liǎng tiáo lù), hanyoyi biyu.
    Ban da wannan kuma, a kan yi amfani da kamla 头 (tóu) don siffanta dabbobi. Ma'anar 头 (tóu) ita ce kai. Don haka, mu kan cewa, shanu 头 uku, 三头牛 (sān tóu niú), wato shanu uku.
  • Daidai kamar harshen Hausa, a kan yi amfani da wasu kalmomi tare don bayyana wani abu. Misali jirgin }asa a cikin Sinanci shi ne 火车(huǒchē), wato“jirgin wuta”. Kazar wuta, 火鸡(huǒjī), wato talo-talo da Hausa. Sa’an nan, “jirgin tururi”, 汽车(qìchē) shi ne mota, kuma “jirgin lantarki”, 电车(diànchē), shi ne motar da ke aiki da wutar lantarki.