Darasi na 15 Cin Kayan Tande-tande da Lashe-lashe

 Hira da CRI
 

Sharhi kan tsinkunan cin abinci da Sinawa ke amfani da su, da kuma wu}a da cokali mai yatsu da Turawa ke amfani da shi. Masana sun yi bincike sun gano cewa, dalilin da ya sanya Sinawa suke amfani da tsinkuna wajen cin abinci shi ne, domin su fil azal manoma ne, akasarin abincinsu ganyaye ne, sabo da haka, ya fi sau}i su yi amfani da tsinkuna wajen cin ganyaye. Amma Turawa, da yake asalinsu makiyaya ne, sun fi dogaro da nama a matsayin abincinsu. Sabo da haka, wu}a da cokali mai yatsu ya fi amfani gare su wajen cin nama.. Sa'an nan kuma, Sinawa kan ci abinci tare. Su kan ]ebi abinci daga faranti guda. Yin amfani da tsinkunan cin abinci na iya kayyade yawan abincin da mutane suka ]iba daga farantin a ko wane karo. Ta haka, yin amfani da tsinkunan cin abinci na iya kare moriyar mutane gaba ]aya gami da rashin raunana moriyar ko wane mutum sosai. Ga mutanen }asashen yammacin duniya, abubuwa na }ara sau}i. Ko wanensu kan ci abinci daga faranti nasa. Kazalika kuma, akwai abubuwan kunya da dole ne a lura da su, kamar kada a ajiye tsinkunan cin abinci a cikin wani kwano mai cike da shinkafa ma}il. Haka kuma, buga kwano da tsinkunan cin abinci ko kuma cokali ya nuna rashin ladabi.