你们喜欢吃辣的吗?Nǐmen xǐhuan chī là de ma?
Kana sha'awar abinci mai kayan yaji?
A darasinmu na al'adun }asar Sin, mun taba ambata cewa, abinci daga Sichuan, da Hunan da wasu larduna yana }unshe da kayan yaji sosai. 'Yan matan Beijing suna matu}ar son abinci mai yaji. Sabo da haka, ya zama wajibi a san yadda ake tambayar "kana son abinci mai kayan yaji?" da Sinanci. Kana iya cewa, 你们喜欢吃辣的吗? Nǐmen xǐhuan chī là de ma?
你们 nǐmen, ku.
喜欢 xǐhuan, so, ko nuna sha'awa.
吃 chī, cin abinci.
辣的 là de, kayan yaji.
吗 ma, wannan na matsayin alamar tambaya.