Darasi na 14 [ebi da Kanka

 Hira da CRI
 

A ko da yaushe Sinawa su kan yi amfani da kalmar shayi ko kofi domin bayyana bambancin da ke tsakanin al'adun }asashen yammaci da na Sin. Shayi ya kasance abin shan Sinawa a cikin dubban shekarun da suka gabata. Shayi ya samo asali kimanin shekaru dubu biyar da suka gabata. Shayi yana matsayin wata alama ta gabashin duniya, yayin da kofi yake a matsayin alamar yammacin duniya. Yanayi a yankunan kudanci da gabashin Sin ya dace da noman ganyen shayi. A lokutan da, an fitar da shayi zuwa }asashen Asiya da Turai ta wata tsohuwar hanya da ake kira hanyar siliki. A zamanin yau, ana kiran shayi da sunaye daban daban a duniya. A nan }asar Sin dai, ana kiran shayi da suna 茶chá. Idan aka kwatanta da }asashen da ke noman kofi, wanda Sin take nomawa ka]an ne. Masana’antar kofi ta farko a nan }asar Sin an bu]e ta ne a birnin Shanghai a shekarar 1935, amma sai a shekarun 1980 ne Sinawa suka fara nuna sha'awa ga shan kofi.