请你们等一会儿。Qǐng nǐmen děng yíhuìr.
Don Allah ku jira ka]an.
A Beijing za ka iya more abinci mai da]i irin na wurare daban daban na }asar Sin. Akwai fitattun wuraren cin abinci. Amma a wasu lokuta, dole ne sai mun jira sabo da cunkoson jama'a. Musammam lokacin cin abincin rana, wato }arfe 12 zuwa 2. Ko kuma da yamma, da }arfe 5 zuwa 8.
Ta haka an sha gaya maka cewa, don Allah ku jira ka]an. Wato 请你们等一会儿. Qǐng nǐmen děng yíhuìr.
请 qǐng, don Allah.
你们 nǐmen, ku.
等 děng, a jira.
一会儿 yíhuìr, ]an lokaci, gajeren lokaci.