Darasi na 1 Gaisuwa

 Hira da CRI
 

Akwai wasu ]abi’u da mai yiyuwa kun lura da su a baya, wasu mutane su kan ce, 您好nín hǎo wajen gaisuwa, maimakon 你好nǐ hǎo. To, akasari dai ana amfani da 你好nǐ hǎo tsakanin mutanen da tsarar juna, wa]anda shekarunsu na haihuwa suke daidai. Amma idan ka gamu da mutumen da ya fi ka shekaru, sai ka ce, 您好nín hǎo, sabo da nuna girmamawa. Sabo da haka, 您好nín hǎo tana nuna girmamawa ga wanda ake gaisuwa.