Darasi na 1 Gaisuwa

 Hira da CRI
 
  • Barka dai. A Sinanci, akwai hanyoyi da dama da za a iya gai da mutum. Amma wadda aka fi amfani da ita yau da kullum ita ce kalma 你好nǐ hǎo. 你nǐ tana nufin kai ko ke. 好hǎo tana nufin da kyau, wato kyakkyawan hali. Idan aka ha]e wa]annan kalmomi biyu wato 你好nǐ hǎo, zai ba da ma’ana kamar haka: kana ko kina cikin hali mai kyau. Ko kana ko kina cikin alheri. Ana iya amfani da wannan kalmar gaisuwa ta 你好nǐ hǎo a ko wane lokaci, ko wane hali kuma ga ko wane mutum. Ana iya yin amfani da 你好nǐ hǎo ga ba}o ko kuma wanda aka riga aka sani. Idan wani ya ce maka 你好nǐ hǎo, kai ma za ka maimaita abin da ya fa]a, wato in ce, 你好.Nǐ hǎo.
  • Mene ne sunanka? Bayan kun gaisa, kana tunanin yadda za ka tambayi sunansa ko sunanta da Sinanci. To, kana iya tambayar sunan mutum da Sinanci kamar haka 你叫什么名字? Nǐ jiào shénme míngzi? 你nǐ yana nufin kai ko ke. 叫jiào, kira. 什么shénme tana nufin mene ne? 名字míngzi, wato suna. Wajen amsar, mutum yana iya fa]in sunan kawai, ko kuma mutum yana iya }ara da cewa, sunana wane, wato 我叫Wǒ jiào.
  • Ga katin sana’ata. A wannan zamani a nan }asar Sin, mutane suna yawan baiwa juna katunan sana’a yayin da suka sa]u da juna a karo na farko. Yayin da ake mi}awa juna irin wannan kati, a kan ce, 这是我的名片.Zhè shì wǒ de míngpiàn. 这zhè na nufin wannan. 是shì na nufin kasancewa, kuma shi ne ko ita ce. 我的wǒ de a Sinanci tana nufin nawa. 这是我的zhè shì wǒ de na nufin wannan nawa ne. 名片míngpiàn, katin sana’a. 这是我的名片.Zhè shì wǒ de míngpiàn. Wannan shi ne katin sana’ata.
  • Mun da]e ba mu ga juna ba. Misali kai da abokinka,ko ke da }anwarki kun jima ba ku ga juna ba, a Sinanci mu kan ce,好久不见.Hǎojiǔ bújiàn. 好久hǎojiǔ yana nufin lokaci mai tsawo. 不bú na nufin ba ko babu. 见jiàn,gani.