Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha: 'Yantar da kasa ne dalilin matakan soji da ake aiwatarwa a arewacin kasar
2020-11-11 13:20:03        cri

Mahukunta a kasar Habasha sun ce yunkurin 'yantar da kasar ne ya wajibta daukar matakan soji a sassan arewacin kasar. Da yake zantawa da manema labarai game da hakan, kakakin sabon kwamitin kar ta kwana da aka kafa, game da rikicin Tigray Mr. Redwan Hussein, ya ce fatan da ake yi shi ne, matakan sojin su kai ga cimma nasarar ceto kasar daga hargitsi.

Hussein ya kara da cewa, 'yan tawayen Tigray ko TPLF a takaice, sun yi awon gaba da manyan makaman soji, don haka burin gwamnati shi ne tabbatar da cewa, makaman ba su fada hannun wadanda ba su kamata a cikin kasar da ma ketare ba.

Bugu da kari, Mr. Hussein ya ce ya zuwa yanzu, jiragen sama masu kai farmaki na Habasha, na yin barin wuta kan sansanonin 'yan tawayen na Tigray ba tare da wata matsala ba. Ya kuma yi watsi da damuwar da wasu ke nunawa, cewa mai yiwuwa tashin hankulan dake shafar yankin na Tigray, ka iya fantsama zuwa kasashe makwafta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China