Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD na yunkurin tallafawa wadanda rikicin Tigray ya shafa
2020-11-10 11:23:10        cri
MDD da abokan huldarta, za su kasance a yankin arewacin Tigray na kasar Habasha, domin tallafawa sama da mutum miliyan 2 da rikicin yankin ya shafa kai tsaye.

A cewar hukumar MDD mai lura da ayyukan ba da agaji ko OCHA a takaice, jami'an ta za su kasance a ciki, ko kusa da yankin mai fama da tashe tashen hankula, ta yadda al'ummun yankin dake cikin matsananciyar bukata, da wadanda suka gujewa gidajen su, da masu gudun hijira za su samu taimako.

Ofishin OCHA ya ce yankin Tigray na kan iyakar Habasha da Eritrea, kuma akwai mutane da yawan su ya kai kusan miliyan 9 dake zaune daura da yankin, wadanda kuma ka iya fadawa tashe tashen hankula. Kaza lika OCHA ta ce akwai kimanin mutane 6,000, da suka harbu da cutar COVID-19 a yankin.

Bugu da kari, hukumar ta jin kai ta ce yankin Tigray, na kan gaba cikin wurare dake fuskantar annobar farin-dango masu bin yankunan hamada, inda kuma ake hasashen sabon rukunin farin za su aukawa yankin cikin makwanni masu zuwa, don haka OCHA ke tsara dabarun tallafawa mazauna Tigray, ciki hadda kafa asusun tallafawa yankin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China