Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe wasu bata gari yayin luguden wuta
2020-11-09 10:14:22        cri
Rundunar sojin Nijeriya, ta tabbatar da kashe wasu 'yan bindiga yayin wani luguden wuta da ta yi a jihar Kaduna, dake arewamaso yammacin kasar.

Kakakin rundunar John Enenche, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya cewa, an yi luguden wutar ne a wani dajin yankin Kuzo na jihar a ranar Asabar.

Ya ce jirgin yaki mai saukar ungulu da aka tura gudanar da aikin, ya gano 'yan bindigar a wani budadden wuri dake gabas maso yammacin dajin, sai dai, bai bayyana ainihin adadin 'yan bindigar da aka kashe ba.

A cewarsa, 'yan bindigar da suka addabi jihar da yankin arewa masu yammacin kasar, na yunkurin safarar daruruwan dabbobi ta yankin na Kuzo a lokacin da aka yi musu luguden wutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China