Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan bindiga 38
2020-10-27 09:38:28        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun hallaka 'yan bindiga 38, yayin hare-hare da suka kaddamar cikin watan nan na Oktoba, a sassan arewa maso yammacin kasar.

Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar Benard Onyeuko ya fitar, sojojin sun ce sun cafke karin wasu 'yan bindigar, da kuma masu taimaka musu su 198, karkashin shirin da aka yiwa lakabi da "Sahel Sanity". Kaza lika sojojin sun tarwatsa wasu sansanonin bata garin guda 10.

Har ila yau sanarwar ta ce dakarun sojin Najeriyar sun kubutar da wasu mutanen 108 da 'yan bindiga ke tsare da su, yayin ayyukan bincike da gano maboyar 'yan ta'adda.

A daya hannun kuma, sojojin sun dakile hare-haren 'yan bindiga har 47, da kuma yunkurin sace mutane sau 31, yayin da suke matsa kaimin kawar da ayyukan bata gari, daga yankunan arewa maso yammacin kasar, wadanda a yanzu ke fuskantar kalubalen ayyukan muggan bata gari.

Bugu da kari rundunar sojojin ta ce, karshin shirin na "Sahel Sanity", tana fatan kawar da munanan ayyukan 'yan fashin daji, da masu satar shanu, da masu garkuwa da jama'a domin neman kudin fansa, da sauran laifuka masu nasaba da kisan fararen hula. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China