Nurimangul Obulqasim ta taba karatu a cibiyar koyar da ilmin sana'o'i a jihar Xinjiang. Yanzu tana matsayin direkta mai kula da harkokin mata a wani kyauye, ta tuna cewa, saboda matukar talauci ba ta samu ilmi sosai ba. Karon farko da ta shiga wannan cibiyar, ta yi mamaki sosai saboda ganin na'urorin zamani da take da su. Ta ce, wannan cibiya makaranta ce mafi kyau a gare ta. Daliban cibiyar suna samun darasuna 6 a ko wace rana daga Litinin zuwa Juma'a, inda suke koyon daidaitaccen Sinanci da ilmin doka da shari'a da fasahohin sana'o'i da kawar da tsattsauran ra'ayi. A lokacin hutu na Asabar da Lahadi kuma, su kan je ayyukan addini.
Ta ce, wasu kafofin yada labarai sun ba da labari cewa, cibiyar ta cire kodar dalibanta da tilasta su aske gashinsu, wanda ta bayyana a matsayin maras tushe. Ta ce tana maraba da wadannan kafofin yada labarai su ziyaraci Xinjiang don ganewa idanunsu hakikanin halin da ake ciki, da ma tattaunawa da daliban da suka taba samun ilmi a wannan cibiya. (Amina Xu)