Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Almira Ablat: Na Gamsu Da Zaman Rayuwata Yanzu A Matsayin Malama
2020-11-04 11:29:04        cri

Almira Ablat, 'yar gundumar Wensu dake yankin Aksu na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, wata malama ce a cibiyar horaswa. Tana alfahari sosai da zamanta malama, kuma shi ne mafarkinta tun tana karama.

Amma, Almira Ablat ta taba jefa kanta cikin tsattsauran ra'ayi a shekarar 2016, lokacin da ta halarci wani bikin aure. Tun daga wancan lokaci ta fara kallo ko sauraron bidiyoyin masu yada tsattsauran ra'ayi. Saboda haka, zaman rayuwata ya canja, ba ta yin wake-wake ko raye-raye kamar yadda ta saba a da, tana son kisan kai don sadaukar da kanta ga addini.

Almira Ablat ta yi sa'a ta samu damar shiga cibiyar koyar da ilmin sana'o'i dake wurin, ta koyi dokar aure da dokar ba da tabbaci ga mata da dai sauran dokoki. A cewarta, wadannan ilmi sun fahimtar da ita ainihin doka da shari'a. Ta fahimci cewa, duk abubuwan da wadannan masu tsattsauran ra'ayi suka zuga ta ta yi, sun sabawa doka. Da ba ta shiga wannan cibiya ba, da ta tafka laifi.

Almira Ablat ta ce, malamai a wannan cibiya na da hikima da kuma kwarewa matuka, sun koya mata daidaitaccen Sinanci. Ta nemi gurbin aiki a wata cibiyar horaswa dake biyan albashin kimanin RMB Yuan 3500 a ko wane wata.

Almira Ablat ta ce, yanzu tana more zaman rayuwarta sosai, kuma tana da imanin yin zaman rayuwa mafi nishadi nan gaba. Kuma za ta gayawa dalibanta labarinta don kada su kauce hanya da samun damar rayuwa lami lafiya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China