Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace Amurka ta kalli kanta kafin ta zargi wasu
2020-09-18 20:33:05        cri

A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai cewa, ya dace kasar ta Amurka ta yi la'akari kan matakan da ta dauka kafin ta zargi sauran kasashe, alal misali, me ya sa ta fice daga hukumar lafiya ta duniya? Me ya sa ta janye daga yarjejeniyar Paris da yarjejeniyar nukiliyar Iran? Haka kuma me ya sa ta sanar da cewa, ta ki amince da hukuncin da kungiyar cinikayyar duniya ta yanke da kudurin babban taron MDD kan annobar cutar numfashi ta COVID-19?

A jiya Alhamis, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka David R. Stilwell ya zargi kasar Sin yayin taron sauraron ra'ayin jama'a na majalisar dattijan kasar, cewa wai kasar Sin tana kawo barazana ga tsarin kasa da kasa.

Kan wannan batu, Wang Wenbin ya bayyana cewa, wace ta fice daga kungiyar kasa da kasa ko kuma janyewa daga yarjejeniyar da kasashen duniya suka daddale, ita ce ke lalata tsarin kasa da kasa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka domin kare tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, wanda aka kafa bisa tushen dokokin kasa da kasa, ana sa ran kasashen duniya za su yi kokari tare domin nuna adawa ga bangaranci, haka kuma su gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar bil Adam.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China