Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare karo na 3
2020-11-02 11:16:29        cri
An shiriya tsaf kan bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare karo na 3 da zai gudana. Yawan fadin shagunan ya karu da kashi 14% bisa na bikin da ya gabata. A karon farko, kimanin kamfanoni mafi karfi 50 daga cikin kamfanonin 500 dake sahun gaba a duniya za su shiga bikin. Ban da wannan kuma, goman kamfanoni sun kulla yarjejeniyar shiga bikin a cikin shekaru 3 masu zuwa, ta hakan za a baje daruruwan sabbin kayayyaki da fasaha da hidimomi a duniya karon farko a nan kasar Sin.

Bukukuwa biyu da suka gabata, an zura ido sosai kan wasu manyan injuna masu kwakwalwa. A wannan karo kuma, kamfanoni daban-daban za su kara gabatar da sabbin injuna a wannan fanni.

Bayan bude wannan gaggarumin biki, kamfanoni daban-daban za su baje kayayyakinsu a Shanghai, don more damammaki da zarafin bunkasuwar kasuwannin kasar Sin. Kuzarin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da alkawarin da Sin take yi na kara bude kofa ga waje, ya baiwa kamfanonin kasashen waje kwarin gwiwar habaka zuba jari a kasar da ci gaba da raya sha'anoninsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China