Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Kashgar na jihar Xinjiang zai tabbatar da kyautata zamantakewar al'ummarsa
2020-10-27 13:53:54        cri

Mataimakin sakatare janar na gwamnatin yankin Kashgar na jihar Xinjiang, Eset Ulayin, ya bayyana a jiya cewa, za a mayar da hankali wajen kyautata zamantakewar mutanen dake cikin bukata tare da shawo kan matsaloli da wahalhalun da suke fuskanta.

Da yammacin jiyan ne kuma ofishin yada labarai na gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ya gudanar da taron manema labarai karo na biyu kan aikin kandagarki da takaita yaduwar COVID-19 a gundumar Shufu na yankin Kashgar. Eset Ulayim, ya ce bayan barkewar COVID-19 a Shufu, nan take yankin Kashgar ya kaddamar da matakan kariya na gaggawa domin shirya kayayyakin da ake bukata na kandagarki da taimakawa jama'a, ya kara da cewa, dongane da tabbacin samar da kayayyakin kandagarki, yankin Kashgar ya yi namijin kokari wajen samarwa da rabawa da adanawa da kuma tabbatar da wadatuwarsu. Kayayyakin sun hada da na kashe kwayoyin cuta da magunguna da kayayyakin aiki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China