Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi asarar rayuka 69 a zanga-zangar adawa da zaluncin 'yan sanda a Najeriya
2020-10-24 17:08:08        cri
Jimilar mutane 69 ne suka rasa rayuka a zanga-zangar neman kawo karshen zaluncin 'yan sanda a Najeriya.

Wata majiya daga ofishin shugaban kasar ce ta sanar da wannan adadi ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a jiya Juma'a.

Rahotannin sun ce shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ne ya bayyana wannan adadi ga tsoffin shugabannin kasar a wani taron bidiyo da aka gudanar don neman dabarun daidaita yanayin tsaro a kasar.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce wannan jimillar ta kunshi wadanda suka mutu a cikin fararen hula, da 'yan sanda, gami da sojoji, tun bayan kaddamar da zanga-zangar, a ranar 7 ga watan nan. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China