Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin bukatun neman hakkin mallakar fasahar AI a kasar Sin ya karu da sama da kaso 52
2020-10-23 11:22:42        cri

Kasar Sin ta karbi sama da bukatu 30,000 na neman hakkin mallakar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a 2019, adadin da ya karu da kaso 52.4 a kan na sheakarar 2018.

A cewar wani rahoto da ya mayar da hankali kan samar da sabbin fasahohin AI na zamani, da aka fitar jiya a taron kirkire-kirkire na Pujiang da ya gudana a Shanghai, kasar Sin ta wallafa jimilar mukalu 28,700 a kan fasahar AI a 2019, adadin da ya karu da kaso 12.4 a kan na 2018.

Manazarta daga cibiyoyi sama da 10, ciki har da kwalejin raya kimiyya da fasaha ta kasar Sin ne suka hada rahoton, wanda ya kunshi shirin da kasar Sin za ta aiwatar kan samar da sabbin fasahohin AI da kuma bayyana kalubale da nau'o'in da za a samar a nan gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China