Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Yawan amfani da fasahar adana bayanai a yanar gizo ya ninka da sama da sau daya a 2019
2020-09-14 10:20:39        cri
Wani rahoto da cibiyar bincike ta kamfanin Tencent na kasar Sin ta fitar, ya nuna cewa, alkaluman auna yawan amfani da fasahar adana bayanai a rumbunan adana bayanai na yanar gizo a Sin, sun ninka da sama da kaso 118% a shekarar 2019.

Rahoton ya nuna cewa, sassan rayuwa da dama na gargajiya, a yanzu na amfani da fasahar sadarwa wajen gudanar da ayyukan su. Rahoton ya nazarci alkaluman yawan bayanai da ake tattarawa a rumbunan adana bayanai na yanar gizo, game da birane da rukunonin birane dake sassan kasar.

Fannonin masana'antu kamar na kera ababen hawa, da na watsa shirye shiryen radio da talabijin, da masu hada hadar yawon bude ido, na kara amfani da fasahar, inda adadin yawan amfani da fasahar ya ninka da rubi sama da 4, yayin da suke kara zamanantar da hanyar ajiyar bayanan su.

Kaza lika a cewar rahoton, wannan adadi ya karu a bana, idan an kwatanta da shekarar bara, yayin da manhajojin ayyuka daga nesa, kamar na koyar da ilimi ta yanar gizo ke kara fadada bukatar hakan.

Sama da rabin biranen kasar Sin, sun samu karuwar amfani da wannan fasaha ta tattara bayanai da kason da ya haura ninki daya, yayin da karin sassan kiwon lafiya da ilimi, da na inganta ba da hidimomin rayuwa ke kara fadada bukatar su a fannin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China