Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a zurfafa hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha
2020-10-22 12:27:15        cri

Ministan kula da kimiyya da fasaha na kasar Sin, Wang Zhigang, ya yi kira da a fadada tare da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha.

Ya ce yayin shirin raya kasa na shekaru 5, karo na 13, kasar Sin ta yi ta shiryawa da inganta kirkire-kirkire da nufin bunkasa shi a duniya, sannan ta samar da wani tsarin hada kirkire-kirkire a duniya.

Ya ce a fannin kimiyya da fasaha, kasar Sin ta hada hannu da kasashe da yankuna 161, sannan ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 114 tare da shiga hukumomin kasa da kasa da kawancen kasashe sama da 200.

Ya ce cikin shirin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kasar ta tallafawa matasa masana kimiyya daga kasashe daban-daban da yawansu ya zarce 8,300 samun aiki a kasar Sin, ta kuma horar da mutane 180,000 tare da kaddamar da dakunan gwaje gwaje na hadin gwiwa guda 33 na hanya daya da ziri daya. Har ila yau, ta gina cibiyoyin raya kimiyya da fasaha na hadin gwiwa da kasashe 8. Baya ga haka, ta gina dandali 5 na yayata fasahohi a matakin kasa, haka zalika ta kaddamar da cibiyar hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire tsakaninta da nahiyar Afrika.

Ya kara da cewa, karuwar adadin Sinawa masana kimiyya da manazarta, ya ba da gudunmuwa wajen warware muhimman batutuwan da suke ciwa duniya tuwo a kwarya. Ya ce kasar Sin ta raba dabarunta na kandagarki da takaita yaduwar COVID-19 ga al'ummun duniya ta hanyar gina budadden dandalin ba da hidimomin kimiyya, wanda ya amfanawa kasashe da yankuna 175, aka kuma sauke har sama da sau miliyan 160. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China