Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun kasashen waje dake Sin sun je kauyen Chixi domin nazarin hanyar yaki da talauci
2020-10-17 20:38:46        cri

Jakadun kasashen waje da manyan baki da suka halarci taron karawa juna sani kan dabarun yaki da talauci da hakkokin dake wuyan jam'iyyun siyasa, wanda ya gudana ta kafar intanet a lardin Fujian na Sin sun je kauyen Chixi na kabilar She na garin Panxi na birnin Fuding dake lardin Fujian a ranar 13 ga wata, domin nazarin hanyar yaki da talauci da ake bi a wurin.

Da shigarsu kauyen, ni'imtattun wurare iri iri, kamar su duwatsu masu launin kore da ruwa mai tsabta suka ja hankalinsu matuka, inda kuma suka nuna sha'awa kan gidajen da aka gina daga farkon titi zuwa karshensa a kauyen.

 

A cikin shekaru sama da 30 da suka gabata, manoman kauyen sun yi amfani da hanyoyi daban daban yayin da suke yaki da talauci domin fita daga kangin talauci a kauyen. Misali neman samun tallafin kudi, da kaura zuwa wani wuri na daban domin samun aikin yi, da raya aikin yawon shakatawa, da kuma raya sana'o'i daban daban da suka dace da yanayin kauyen, yanzu haka sun riga sun cimma burin fita daga talauci ba tare da gurbata muhalli ba.

 

Bayan ya saurari rahoton da aka gabatar kan yadda suka yaki da talauci a kauyen, jakadan jamhuriyar kasar Bulgaria Grigor Porozhanov ya bayyana cewa, kasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta matuka wajen yaki da talauci, kuma yana ganin cewa, ziyararsu a kauyen Chixi tana da babbar ma'ana, inda ya bayyana cewa, "Muna bukatar cudanya da musanyar ra'ayoyi da tattaunawa kan muhimman batutuwa, kuma ya dace a raba fasahohin da aka samu. Talauci abokin gaba ne na daukacin bil adama, kuma kusan daukacin kasashen duniya suna fuskantar wannan matsala, shi ya sa ya kamata a ci gaba da kokari domin kawar da talauci daga duk fannoni."(Jamila)

 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China