Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsaron MDD ya yi maraba da fadada tsarin mika mulki ga farar hula a Mali
2020-10-16 12:21:02        cri

A jiya Alhamis, kwamitin tsaron MDD ya bayyana gamsuwa game da fadada tsarin mika mulki ga farar hula a kasar Mali, yana mai fatan dukkanin sassan da batun ya shafa, za su kiyaye yarjejeniyar da aka cimma.

Cikin wata sanarwar shugaba da kwamitin ya fitar, wadda jagorar sa ta watan Oktoba Vassily Nebenzia ta gabatar, mambobin kwamitin 15, sun jinjinawa nadin shugaba, da mataimakin shugaba, da firaministan gwamnatin ta Mali. Kaza lika majalissar ta gamsu da fitar da yarjejeniyar gudanar da gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Har ila yau, sanarwar ta yi maraba da sakin jami'an da aka tsare bayan juyin mulkin kasar, kamar dai yadda kungiyar ECOWAS ta bukata. Kana kwamitin ya bukaci a gaggauta nada mambobin hukumar zartaswa ta gwamnatin rikon kwaryar.

A daya bangaren kuma, kwamitin tsaron MDDr ya yabawa kwazon ECOWAS, game da shiga tsakanin ta a Mali, yana mai goyon bayan sanarwar da ECOWAS din ta fitar ranar 5 ga watan nan, game da shirinta na dagewa Mali takunkumai.

Kaza lika kwamitin ya amince da dage takunkumin da hukumar kungiyar AU mai lura da zaman lafiya da tsaro ta kakabawa kasar na shiga a dama da ita a harkokun AU.

Daga nan sai mambobin kwamitin tsaron suka bayyana burin su, na ganin an aiwatar da yarjejeniyar mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula, ta hanyar gudanar da babban zaben kasa nan da watanni 18 masu zuwa. Kwamitin ya kuma yi fatan ganin an gudanar da sahihin zabe, a bayyane, mai cike da adalci, wanda zai wakana cikin kyakkyawan yanayi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China