Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ECOWAS: A gaggauta kawo karshen takaddamar siyasar kasar Mali
2020-09-16 10:46:29        cri
Shugaban karba karba na kungiyar raya yammacin Afirka ECOWAS, kuma shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar, da su yi hadin gwiwa wajen gano bakin zaren takaddamar siyasa dake addabar kasar Mali.

Shugaba Akufo-Addo, ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin bude taron shugabannin ECOWAS, inda ya ce akwai bukatar gaggauta warware rigingimun dake barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin yammacin Afirka, da ma sauran yankunan nahiyar.

Akufo-Addo, wanda ke jagorantar taron kungiyar a karon farko, ya ce halin da ake ciki a Mali, na bukatar a gaggauta kawo karshen rashin jituwa.

Ya ce "Ina fatan ganawa ido da ido tsakanin wakilan kungiyar mu mai mambobi 15, da bangaren sojojin dake jagoranci a Mali, zai ba mu babbar dama ta shawo kan yanayin da ake ciki", a kalaman shugaban na Ghana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China