Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gudanar da taron tattauna kan hadin kan addinai daban-daban don yakar COVID-19
2020-10-13 11:31:41        cri
Jiya Litinin, kwamitin addinai daban-daban, da zaman tare cikin lumana na kasar Sin, ya kira wani taro ta kafar bidiyo mai taken "Hadin kai da cin gajiya tare don rarraba fasahar yakar COVID-19 tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban". A gun taron, an gabatar da dabarun da Sin take aiwatarwa wajen yakar cutar, da yin kira da a yi kokarin tabbatar da kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da ma nuna goyon baya ga hadin kan kasa da kasa ta fuskar yakar cutar.

Wakilan kungiyoyin addinin Buddha, da Tao da Musulunci, da Kiristoci 'yan katolika sun halarci taron. Kaza lika akwai wakilai daga kungiyoyin addinai na kasa da kasa, da na nahiyar Asiya da suka halarci taron, tare da ba da jawabi, ciki hadda walilai daga Austriliya, da Bangladesh, da Indonesiya, da Japan. Sauran sun hada da wakilan kasashen Korea ta kudu, da Malaysia, da Philiphines, da Pakistan, da Italiya, da Belgium, da Birtaniya da ma na sauran kasashe 11. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China