Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta yi kokarin ingiza hadin kan duniya wajen yakar cutar COVID-19
2020-09-08 20:36:52        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shedawa manema labarai a yau Talata cewa, yanzu haka cutar COVID-19 na ci gaba da dabaibaye dukkanin fadin duniya. Don haka kasar Sin ke fatan ci gaba da ingiza hadin kan kasa da kasa, bisa tunanin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, don goyon bayan hukumar WHO, ta yadda za ta taka rawa wajen jagoranci aikin yaki da cutar, da ma more dabaru, da fasahohin kasa da kasa, da ci gaba da baiwa kasashe da suke da karancin karfin tinkarar cutar taimako, ta yadda dukkanin sassan duniya za su cimma nasarar wannan yaki.

Wasu rahotanni ne cewa, jami'in hukumar ta WHO Bruce Alyward, ya bayyana a jiya Litinin cewa, matakin Sin na cimma nasarar dakile cutar, ya zama abu mai matukar faranta rai. Kuma ya yi kira ga kasashen duniya, da su koyi darasi daga kasar Sin a fannoni uku, wato kafa manyan ababen more rayuwa a fannin kiwon lafiya ga dukkanin al'umma, da karawa jama'a kwarin gwiwa wajen sauke nauyin dake wuyansu, da ma kara karfin ba da jiyya a dukkanin fannoni, don tinkarar cutar a dogon lokaci.

(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China